Najeriya: Horon musamman na kaifafa kwazon sojoji
March 26, 2025Ministan Tsaron Nigeria Alhaji Badaru Abubakar ya bayyana sabbin dabarun da gwamnatin kasar ta aiwatar ta hanyar horar da sojojin 800 dabarun yaki na zamani da tsare fararen hula da garuruwansu daga duk wata barazana ta mahara da ke addabar mazauna karkara da manoma.
Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da ake samun nasarar rage hare haren ‘yan bindigar daji da sauran ‘yan ta'adda da ke addabar mazauna karkara da sauran hanyoyin sufuri a sassa daban daban a fadin kasar
Ya ce mun zo kaduna ne domin kaddamar da shirin farko na horar da dakarun soji 800 sabbin dabarun yakin zamani da suka sha banbban da na shekarun baya
Alhaji Badaru ya nunar da cewa kwarrarru aka dauko daga wasu kasashen Turai bakwai domin koya wa sojojin Najeriya dabarun zamani na yakin kundun-bala da hanyoyin kare mutanen gari da inda suke zaune daga hare haren ‘yan ta'adda da sauran mazauna garuruwan da ke a dokar daji
Ya ce wannan horo na da matukar fa'Ida a kokarin da hukumomi da kungiyoyin wanzar da zaman lafiya ke yi wajen murkushen dukkanin fitintinun da ke da nasaba da tabarbarewar tsaro da sauran tashe tashen hankula da ke janyo asarar rayuka da dumbun dukiyar al'ummar kasa
Wadannan Rukunin sojojin da suka fara daukar horo, su ne na farko a Najeriya da ake sa ran za su sami horo kan wadannan matsaloli domin taimaka wa wajen kawo karshen dukkanin tashe tashen hankula da ke da nasaba na satar mutane da kuma garkuwa da su don neman kudin fansa
Ministan tsaron ya bayyana cewa, akalla dakarun tsaro 2400 ne ake sa ran horarwa a shirin baki daya,wadanda kuma ake sa ran za su taka muhimmiyar rawa wajen dakile yaduwar ayyukan miyagun mutane da ke hana zaman lafiya da sauran ayyukan mahara da ke addabar mazauna karkara
Bugu da kari, Ministan ya bayar da haske kan irin nasarorin da gwamnatin ke samu wajen rage hare haren kan fararen hula, lamarin da suka farfado da harkokin kasuwannin karkara da zirga zirgar sufuri da harkar noman rani da damuna a irin wannan lokaci
Alhaji Badaru Abubakar ya yi haske kan inda aka kwana wajan kama Fitattchen dan fashin –daji da ke addabar al'ummar zamfara da katsina da sauran makarrabansa
Ya ce ina tabbatar wa jama'a cewa, jami'an tsaro na bin dukkanin hanyoyin da suka chanchanta domin kama Bello Turji
Duk da irin na mijin kokarin da suke yi na kawo karshen wannan fituna, kungiyar yan sintiri da kasa na fatan ganin an taimaka mata da kayayyakin aiki domin taimakawa hukumomi magance wannnan lamari ganin irin yadda suka jajircewa wajen shiga daji kama bata-gari da sauran masu hana zaman lafiya a cikin kasar
Navy Captain Umar Bakori shi ne shugaban kungiyar yan sintiri da ke janyo hankalin hukumomi wajen tallafa wa ‘yan sa-kai da kayayyakin aiki domin bada gudunmawa wajen dakile ayyukan yan fashin daji da masu sata da garkuwa da mutane don neman kudin fansa.