Najeriya: Sulhu tsakanin ASUU da gwamnati ya gagara
August 17, 2022Wannan taron da aka yi tsakanin jami’an gwamnatin Najeriyar da na kungiyar malaman jamio’in gwamnatin kasar a cike da fata da samun mafita a wannan zama, saboda an yi shi ne a karkashin wani sabon kwamiti da gwamnatin ta kafa a kokarin na hanzarta shawo kan matsalar yajin aikin. To sai dai zaman nasu sun kasa cimma matsaya abin da ya nuna ci gaba da yajin aiki. Watanni shida kenan dai kungiyar malaman jami’oin tana cikin yajin aiki wanda ya kai ga gurgunta daukacin karatu a jamio’in gwamnati a wannan sherar. Yajin aikin da suka fara a ranar 14 ga watan Faibairu bana bisa bukatun da suka hada da amfani da manhajar biyan malaman jamio’in albashi ta Utas maimakon IPPIS da gwamnatin ta dage, da biyan Naira triliyan 1.1 na asusun farfado da jamio’in. Maimakon duba batutuwan sai jami’an gwamnati suka je da kokon bara ga kungiyar ta yi hakuri ta janye yajin aikin.
Yajin aikin ya janyo tabarbarewar al'amuran illimi a Najeriya
Kwararru a fannin ilimin dai na nuna damuwa a kan illar da ci gaba da yajin aikin ke yi ga tsarin karatu a Najeriyar. Bayanai na nuna cewa sau 16 kenan kungiyar malaman jamio’in gwamnati a Najeriya suna daka yaji suna sha a shekaru 23 a kasar abin da ya shafi karatun boko na jamio’in gwamnati. Wannan ya sanya iyaye da dama tura dalibansu makarantu na kudi a Najeriyar da kasashen waje, yayan marasa galihu kuma na gida a zaune suna jiran tsammanin warabbuka.