Najeriya da dakatar da bai wa dalibai tallafin karatu a waje
May 8, 2025Talla
A hukumance, Najeriya ta sanar da kawo karshen ba da tallafin karatu ga daliban kasar da ke karatu a kasashen duniya, tana mai danganta hakan da ingantuwar ilimin da ake samu a cikin kasa da ma karancin kudade da ake fama da shi.
Musamman ministan ilimi na kasar, Morufu Olatunji Alausa ya ce dukkannin kwasa-kwasan da 'yan Najeriyar ke zuwa wasu kasashe domin nazarin su, akwai su a cikin jami'o'i da ma kwalejojin fasaha masu nagarta da ake da su.
Ministan ya ce kudaden da ake kashewa wajen daukar nauyin karatun daliban a ketare, zai fi dacewa a sanya su wajen inganta jami'o'in da kwalejojin da ake da su.
Najeriya dai na fama da matsalolin tattalin arziki sakamakon matakan da shugaban kasar Bola Tinubu ya dauka da sunan sauye-sauye.