Ina makomar matatun man fetur din Najeriya?
July 18, 2025An dai kashe dalar Amurka miliyan dubu kusan 20 da sunan gyaran matatun guda hudu, ba tare da kai wa ya zuwa cimma bukata a bangaren mahukunta Najeriyar ba. A makon jiya ne dai kamfanin mai na kasar NNPC ya bayyana aniyarsa ta cefanar da matatun da aka kashewa kudin da ke da daman gaske, amma kuma har ya zuwa yanzu ke cikin halin suma.
Karin Bayani:Matsalar matatun mai na boge a Najeriya
Matakin da ga dukkan alamu, ya harzuka masu adawar Najeriyar da ke fadin a bincika kafin cinikin matatun da suka lamushe sama da dalar Amurka miliyan dubu 20 a shekaru 15 din da suka gabata. Ko cikin watan jiya dai sai da ta kai ga Hukumar Yaki da Cin-hanci ta Najeriyar EFCC, kama tsohon jami'in kudin kamfanin NNPC Umar Ajiya kan zargin badakala da kudin gyaran matatun da suka kai dalar Amurka miliyan dubu bakwai da doriya.
Jam'iyyar ADC da ke sahun gaba cikin batun adawar, ta ce ba hali ga Abujar yin cinikin ba tare da bin diddigin kudin da suka bi ruwa wajen cinikin matatun ba. Kokarin wakaci ka tashi ko kuma neman a yadda kwallon mangoro a bangare na masu mulkin Tarayyar Najeriyar dai, tashi na matatun hudu na iya kai wa ya zuwa babban tasiri cikin kasar da ke dada dogaro da matatar man Dangote. An dai dauki lokaci ana kallon matatun hudu da zama kafa ta wasoso, a tsakanin 'yan bokon Najeriyar a lokaci mai nisa.
Karin Bayani: Ko NNPC za ta kyale matatar Dangote?
Matatar man ta Kaduna dai ga misli, ta yi aikinta na karshe a cikin watan Agustan 2015, kuma ta lashe kudi maras adadi a shekaru 10 da ta dauka tana ta kokarin sake tashi. Ibrahim Shehu dai kwarrare ne ga tattali na arziki da kuma ya ce, ba hujjar ci gaba da rike matatun a bangaren masu mulki na kasar. Matatun hudu dai na da karfin tace ganga dubu 445 kusan kullum in sun kai ga fara aikin nasu, adadin kuma da ke iya mai da daukacin kasar ta kan gaba wajen tace danyan man fetur a nahiyar Afirka.