Bincike kan rahoton zubar wa mata ciki
February 1, 2023Talla
Rahotanni daga Najeriya na cewar hukumar kare hakkin bil Adama ta kasar, ta kafa kwamiti na musamman da zai yi bincike a kan zargin da ake yiwa rundunar sojojin kasar da zubar da ciki ga matan da Boko Haram suka sace a shiyar arewa maso gabashi.
Rundunar sojin Najeriyar dai tun da rahoton ya fito suka yi watsi da shi suka kuma ce ba za su gudanar da wani bincike ba.
Hukumar ta NHRC ta ce a makon da ke tafe za ta kaddamar da kwamitin da zai yi wannan aikin.
Kwamitin na mutum bakwai zai sami jagorancin Justice Abdu Aboki da wasu tsaffin manyan sojoji da suka yi ritaya. Sama da mata dubu 10 ne ake zargi an zubar musu da cikin da ake zargin mayakan Boko Haram suka yi musu ta hanyar auren a dole ko kuma fyade.