Gaza: Trump na sa ran za a cimma yarjejeniya a wannan mako
July 7, 2025Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya yi imanin cewa da akwai 'dama mai kyau' ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da kungiyar Hamsa a cikin wannan mako, wadda za ta ba da damar sakin ragowar mutanen Isra'ila da aka yi garkuwa da su a zirin Gaza da kuma mika gawarwakin wadanda suka mutu.
Furucin na shugaban Amurka na zuwa ne a daidai lokacin da wakilan Hamas da na Isra'ila suka fara tattaunawa a birnin Doha bisa shiga tsakanin Qatar, a yayin kuma da ake dakon isar Benjamin Netenyahu birnin Washington a wannan Litinin, inda zai da Shugaba Trump.
Karin bayani: Trump ya sanar da cewar ana shirin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza
Ganawar ta Trump da Netenyahu za ta mayar da hankali kan shawarar Amurka na tsagaita wuta na tsawon kwanaki 60 a zirin Gaza wanda yakin da aka shafe watanni 21 ana gwabzawa ya daidaita.
Sai dai a ranar Asabar an jiyo firaministan Isra'ila Benjamin Netenyahu na cewa ba za su amince ba da wasu canje-canje da Hamas ta bukaci a yi wa daftarin da Amurka ta gabatar, musamman ma janyewar sojojin Isra'ila kwata-kwata daga dan karamin yankin na Falasdinu.