Mutuwar Sarkin Zuru na jijjiga 'yan Najeriya
August 17, 2025Allah ya yi wa sarkin Zuru Manjo Janar Muhammad Sani Sami na biyu ma ritaya rasuwa. Tuni mahukuntan jihar Kebbi suka tabbatar da rasuwar a wannan Lahadi. Mariganyi Manjo Janar Muhammad Sani Sami na biyu mai ritaya rasu ne a jiya Asabar da yammaci bayan jinyar da ya yi a wani asibitin na birnin Landan.
Rasuwar Buhari ta kawo 'yan siyasar Najeriya waje guda
An haifi marigayi Sarkin a shekarar 1943, kafin daga bisani ya shiga aikin soja a 1962, ya kuma taba rike manyan mukamai da dama na kananan da manyan sojojin Najeriya, ciki har da gwamnan Bauchi a lokacin mulkin sojan kasar a 1984 zuwa da 1985, kafin ya yi ritaya a shekarar 1990.
Muhammadu Buhari ya rasu yana da shekaru 82
Manjo Janar Sami na biyu ya rasu yana da shekaru 81 a duniya ya kuma bar mata hud da 'ya' 'ya bakwai. Nan gaba ake sa ran isowar gawar mamacin a Najeriya kafin a sanar da lokacin da za a yi mata jana'iza