Mutum shida sun mutu a turmutsitsin wurin bauta a Indiya
July 27, 2025Akalla mutum shida sun mutu a wani turmutsitsi da ya auku a wani shahararren wurin bauta na mabiya addinin Hindu a arewacin Indiya.
Hukumomin yankin sun sanar a ranar Lahadi cewa akwai mutane da dama da suka jikkata sakamakon fitar dango da masu neman tabarruki suka yi a wajen bautan a ranar Lahadi.
Turmutsitsi ya kashe masu bikin wanke zunubi a Indiya
Lamarin ya faru ne a birnin Haridwar, inda ake yawan zuwa bauta bayan wani layin wutar lantarki mai karfin gaske ya fado a kan wata hanya kusa da wurin bautan.
Lamarin ya jefa masu ibada da dama cikin firgici inda mutane suka rika neman tsira da rayukansu.
Wani babban jami'in gwamnati a jihar Uttarakhand, Vinay Shankar Pandey ya tabbatar da mutuwar mutane shida, ya kuma ce masu ibadar sun fara guje-guje don tsira bayan faruwar lamarin.
Mutum 46 sun mutu a bikin wankan tsarki na addinin Hindu
Jami'an yankin sun ce dubban masu ibada ne suka taru a wajen da ke kan tsauni, wanda ya shahara wajen karbar bakuncin masu ibada na Hindu, musamman a karshen mako da kuma ranakun bukukuwa.