Mutum daya ya tsira a hatsarin jirgin saman Indiya
June 12, 2025Hukumonin Indiya sun tabbatar da cewa mutum daya dan kasar Burtaniya ya tsira da ransa daga hatsarin jirgin saman da ya auku da safiyar yau Alhamis.
Ministan cikin gida na Indiya Amit Shah ya tabbatar da cewa ya gana da mutumin da ya tsira a asibiti kuma likita ya fada mishi cewa ya dubi lafiyar mutumin mai suna Vishwashkumar Ramesh.
Mutumin ya tattaunawa da 'yanuwansa daga asibiti inda ya ce musu jikinsa da sauki kamar yadda wani dan uwansa ya tabbatar wa BBC.
Akalla fasinjoji 200 sun rasu a hatsarin jirgin saman Indiya
Wani babban jami'in 'yansanda a birnin Ahmedabad inda hadarin ya auku Vidhi Chaudhary, ya ce akwai wasu dalibai da lamarin ya rusta da su kasancewar jirgin ya fadi ne a kan dakunan kwanan dalibai.
Ya kuma kara da cewa akasarin gawarwakin da aka zakulo sun kone ta yadda ba lallai ne a iya gano su wane ne ba.
Jirgin da aka harba duniyar Venus ya fado bayan shekaru 50
Da safiyar Alhamis ne dai jirgin saman indiya na Boeing 787 dauke da fasinjoji 242 ya yi hadari bayan tashi daga birnin Ahmedabad da ke arewa maso yammacin Indiyar zuwa birnin Gatwick na Burtaniya.