Najeriya: Mutum 13 sun mutu a hatsarin kwale kwale
July 28, 2025Talla
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Niger da ke Najeriya, NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane 13 sakamakon kifewar wani kwale-kwale a karamar hukumar Shiroro. Kakakin hukumar, Ibrahim Audu Husseini ya ce an ceto mutane 26 daga cikin fasinjoji 39 da ke cikin kwale-kwalen.
Karin bayani: Kwale-kwale dauke da mutane 200 ya kife a tsakiyar Najeriya
A yayin da suke aikin ceto a karshen mako, jami'an agaji sun bayyana cewa kwale-kwalen na kan hanyarsa ne ta zuwa kasuwa, inda kuma ya ke dauke da buhuhunan abinci da kuma wasu dabbobi. Ana yawan samun hatsarin jirgin ruwa a jihar ta Niger, inda ko a watan Nuwambar bara, mutane 27 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka yi batan dabo.