Mutum 100 sun mutu a hare-haren da RSF ta kaddamar a Darfur
April 13, 2025Talla
Sabbin hare-haren da RSF ta kaddamar kan sansanin 'yan gudun hijrar na Darfur ya hakala mutane sama da 100 ciki har da yara kimanin 20 da kuma wasu ma'aikatan agajin jinkai guda tara, a wata sanarwa da ofishin Majalisar Dinkin Duniya ta fitar.
Karin bayani:Sudan: Sojojin gwamnati sun kara samun galaba
Jami'ar MDD da ke yankin Clementine Nkweta-Salami ta ce RSF sun kaddamar da hare-hare a sansanonin 'yan gudun hijra na Zamzam da Abu Shorouk da ke kusa da birnin el-Fasher, da ke lardin Arewacin Darfur.
Karin bayani: Amurka da Saudiyya sun bukaci a kawo karshen yakin Sudan
Birnin el-Fasher na hannun dakarun gwamnati da ke ci gaba da gumurzu da mayakan RSF a filin daga, mutane sama da 24,000 ne suka mutu a birnin a cikin shekaru biyu.