SiyasaAfirka
Mutane uku sun mutu a hadarin helikwafta a Somaliya
July 2, 2025Talla
Rahotani daga birnin Mogadishu na kasar Somaliya na cewa akalla mutane uku ne suka mutu sakamakon hadarin jirgin helikwafta mai dauke da jami'an Hukumar Tarayyar Afirka AU.
Karin bayani: Rikicin Somalia da karewar wa'adin dakarun kungiyar AU
Shugaban Hukumar kula da Sufurin Jiragen Sama na Somalia Ahmed Moalim Hassan, ya ce suna ci gaba da gudanar da bincike kan musabbabin afkuwar hadarin, wanda ke rangadi da dakarun wanzar da zaman lafiya na hukumar AU, a kokarinsu na murkushe mayakan Al-Shabaab.