Mutane sun mutu a mahakar zinare a Sudan
June 30, 2025Rushewar ta faru ne a ma'adinin Kersh al-Feel wanda ke kauyen Howeid a yankin Kogin Nilu na gabas, inda wasu ma'aikata bakwai ma suka jikkata, kamar yadda hukumomi a Sudan din suka tabbatar.
Kamfanin gwamnati mai kula da ayyukan tonon ma‘adinai, ya ce a hukumance ma ya dakatar da aikin hakar zinaren a wannan ma'adanin tun kafin faruwar wannan hadari, tare da yin gargadi ga masu hakar zinaren na gargajiya da su dakatar aiki a wurin saboda hadarin da ke a ciki.
Sudan dai na daga cikin manyan masu hakar zinare a Afirka, amma kuma rashin tsauraran matakan tsaro a ma'adinan gargajiya na haifar da yawaitar hadurran rushe-rushen da ake samu.
A baya ma dai an samu irin wannan hadari a shekarar 2023 inda mutane 14 suka mutu, haka ma a 2021 an rasa rayukan mutane 38 a makamancin wannan hadari.