Mutane da dama sun nutse sakamakon hadarin jirgin ruwa
October 9, 2022Talla
Rahotanni sun yi nuni da cewa jirgin ya kife ne a yayin da yake dauke da fasinja sama da 80 a ranar Asabar, sannan ya zuwa yanzu ba wasu cikakkun bayanai da suka tabbatar da dalilan hadarin.
Wani jami'in agaji Chukwudi Onyejekwe ya shaida wa manema labarai cewa bai wuce mutane 15 kawai da aka gano gawargwakinsu ba bayan iftila'in, kana wasu fasinjoji tara da suka tsallake rijiya da baya na cigaba da samun kulawar likita.
Ana sa ran mutane 76 ne suka halaka a cikin hadarin da wasu masana ke alakantawa da ambaliyar ruwa, wacce alkaluman mahukuntan Najeriya suka nunar da cewa a baya-bayan nan ta halaka mutane 300 wasu fiye da dubu 100 sun rasa matsugunansu a sassa daban-daban na Najeriya.