Mutane 25 aka ceto a Najeriya bayan kifewar jirgi a Sokoto
August 19, 2025Hukumomi a Najeriya sun tabbatar da ceto mutane 25 a raye yayin da ake ci gaba da laluben wasu 25 da ba a kai ga gano su ba, tun bayan kifewar jirgin ruwansu a jihar Sokoto a karshen makon da ya gabata.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar NEMA ta ce zuwa safiyar wannan Talata, babu labarin sauran mutanen 25 da suka lume a ruwan, wadanda ake kyautata zaton rai ya yi halinsa.
Fasinjojin da ke cikin kwale-kwalen mata ne da kananan yara, sai kuma babura da ke kan hanyar zuwa cin kasuwar hatsi ta Goronyo, inda ya kife da su a ranar Lahadi.
Shugaban karamar hukumar Goronyo Zubairu Yari, ya ce karfin igiyar ruwan wani dam da ke kusa da su ne ke ba su matsalar aikin agajin da suke gudanarwa yanzu haka, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito.
Karin bayani:Jirgin ruwa ya kife da mutum 50 a Sokoton Najeriya
A wani labarin kuma kimanin mutane 27 aka tabbatar da mutuwarsu a Jamhuriyar Benin, sakamakon rikitowar motar bas daga kan gada zuwa cikin kogin Oueme, a Kwatano babban birnin kasar, a kan hanyar zuwa Malanville, kamar yadda hukumomin kasar suka tabbatar a yau Talata.
Shugaban hukumar kare lafiyar 'yan kasa Abdel Aziz Bio Djibril, ya ce bayan zakulo motar, sun samu gawarwaki 23 a cikinta, sai wasu 4 da aka dauko gawarwakinsu a cikin kogin daga baya.
Ya kara da cewa an aike da mutane 9 zuwa asibiti bayan ceto su a raye, yayin da ake ta kokarin nemo sauran wadanda suka nutse a ruwan.
Karin bayani:Janar Tiani ya sake zargin Benin da Fransa da daukar nauyin 'yan ta'adda
Motar fasinjojin mallakin kamfanin sufuri na STM, ta taso ne daga birnin Lome na kasar Togo, dauke da mutane 52.