Museveni ya amince kotun soji ta yi farar hula shari'a
June 16, 2025Shugaban kasar Yuganda Yoweri Museveni ya rattaba hannu kan wata doka da ta bai wa kotunan soji damar gudanar da shari'ar farar hula, a cewar majalisar dokokin kasar. Sai dai shugabannin 'yan adawa suka ce wannan mataki ya saba wa hukuncin da wata babbar kotu ta yanke. Dama dai, masu rajin kare hakkin bil adama sun dade suna zargin gwamnatin Yuganda da amfani da kotunan soji wajen gurfanar da masu adawa da shugaba Museveni a siyasance, wanda ya shafe kusan shekaru 40 a kan karagar mulki.
Karin bayani: Shekaru biyu da haramta auren jinsi a Yuganda
Amma masu dasawa da gwamnti sun musanta zargin, suna masu cewa fararen hula da ake yi wa shari'a a kotunan soji, su ne wadanda ke tayar da rikicin siyasa. A farkon wannan shekarar ne kotun kolin kasar Yuganda ta haramta gurfanar da fararen hula a gaban kotun soji, inda ta ce matakin ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar.