Jinkiri ga musayar fursunoni tsakanin Kyiv da Moscow
June 8, 2025A cewar shugaban hukumar leken asirin sojan Ukraine, Kyrylo Budanov komai na tafiya yadda aka tsara duk da rade-radin da ake yi. Tun da fari, jami'an Rasha sun ce suna tsaye da gawarwakin sojojin Ukraine 1,212 da suka mutu, a cikin motoci masu na'urar sanyi, a iyakar kasashen biyu.
Sai dai Budanov ya ce, za a fara aikin dawo da mutanen ne a mako mai zuwa kamar yadda aka amince yayin tattaunawar kai tsaye tsakanin bangarorin biyu a Turkiyya.
Karin bayani: Rasha da Ukraine na zargin juna da jinkirta musayar fursononi
Ana dai ta kwan-gaba kwan-baya kanmusayar gawarwaki da fursononi tsakanin kasashen biyu da ke yaki, inda Rasha ta ce sanar da cewa ta shirya musayar a ranar Asabar yayin da Ukraine ke cewa, Moscow ta yi gaba-gadin kanta ne kawai na zabar rana ba tare da an cimma wata yarjejeniyar tsayar da lokaci a tsakanin kasashen ba.