Muritaniya na kan gaba wajen cin zarafin bakin haure-HRW
August 27, 2025Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Human Rights Watch ta ce dakarun sojin Muritaniya sun yi kaurin suna wajen cin zarafin bakin haure da masu neman mafaka ta hanyar azabtar dasu wasu lokutan har da fyade.
Karin bayani: Gangamin adawa da yakin Isra'ila a Gaza a Muritaniya
Kungiyar ta Human Rights Watch a cikin rahoton da ta fitar mai shafuka 142 ta ce cin zarafin ya faru ne daga shekara ta 2020 zuwa 2025, wanda sojojin ruwa da jami'an hukumar fasakwauri da 'yan sandan kan iyaka suka aikata. Gwamnatin Muritaniya dai ta musanta dukkan zarge-zargen da ake mata na cin zarafin bil Adama, yayinda tarayyar Turai ta jaddada kalaman gwamnatin Nuakschott na martaba 'yancin bani Adama.
Karin bayani: An kwantar da shugaban Muritaniya a asibitin sojin Faransa
A 2024, hukumomin Madrid na kasar Spain sun sanar da cewa mutane akalla dubu 46,843 suka isa tsibirin Canary da ke gabar tekun Spain, duk da cewa adadin yayi kasa zuwa 11,500 daga watan Janairu zuwa Yulin 2025.