Moody's ta rage kuɗin ruwa na wasu ƙasashen Turai
February 14, 2012Hukumar ta ce ta yi haka ne saboda matsalar tattalin arzikin da ke yin barazana ga ƙashen ƙungiyar Tarrayar Turai,tuni dai da ministan kuɗi na ƙasar Faransa Francois Baroin ya ba da sanarwa cewar sun yi la'akari tare da saka ido akan ƙasƙancin da hukumar ta yi akan ƙasar.
Wannan dai ya zone a dadai lokacin da ƙasar Girka ke fama da matsalar tattalin arziki da kuma wasu ƙasashen ƙungiyar tarrayar turai ,wanda yanzu haka ake ci gaba da samun saɓannin tsakanin yan siyasar na Girka akan sabon shirin tattalin arzikin du da ma cewar majalisar dokokin kasar ta kaɗa ƙuria'a amincewa da shirin tsuke bakin aljihun gwamnati.Tun da farko dai hukumar da ke auna ƙarfin ƙasashe na biya bashi wato Standart & Poor's ta rage daraja ƙasar Faransa na biyan bashin ta.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Saleh Umar Saleh