Ministocin Ghana biyu sun mutu a hadarin jirgin sama
August 6, 2025Jirgin ya tashi ne daga Accra babban birnin kasar ta Ghana zuwa lardin Ashanti da ke kudanci, baya ga ministocin biyu akwai wasu manyan jami'an gwamnati guda uku da kuma ma'aikatan jirgin uku.
Karin bayani:Akalla mutum 16 sun rasu a hadarin jirgin sama a Bangladesh
Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar Ghana Julius Debrah, ya sanar da manema labarai cewa mutuwar ministocin biyu babban rashi ne ga daukacin al'ummar kasar baki daya. Ya kara da cewa Shugaba John Dramani Mahama ya aike da sakon ta'aziyya ga iyalan ministocin da sauran wadanda suka mutu a hadarin jirgin.
Karin bayani: An gabatar da rahoton binciken farko na hadarin jirgin Air India
Rahotannin baya bayan nan sun tabbatar da mutuwar Alhaji Muniru Mohammed tsohon ministan noma kuma mataimakin mashawarcin shugaban kasa kan tsaro da kuma mataimakin shugaban jam'iyyar NDC Samuel Sarpong.