Gaza: EU na zaman nazarin matakan ladabtar da Isra'ila
July 15, 2025Ministocin harkokin wajen kasashen Tarayyar Turai na zama a wannan Talata a Brussels domin nazarin matakan ladabtar da Isra'ila kan karya dokokin kare hakkin dan Adam a Zirin Gaza.
Sai dai wasu daga cikin jami'an diflomasiyyar Turan sun ce zai yi wuya minstocin sun yanke shawara ko kuma su zakulo matakai na hakikan da za a dauka ballantana a aiwatar da su.
Wani rahoto da Hukumar gudanarwar EU ta gabatar a karshen watan Juni da ya gabata ya yi nuni da cewa Isra'ila ta saba wa doka mai lamba biyu ta kundin da ta rattaba da Tarayyar Turai a game da mutumta 'yancin dan Adam.
A gefe guda kuma ra'ayoyin kasashen na EU sun rarrabu, inda kasashe da dama ciki har da Jamus suka dage kan cewa Isra'ila na da damar kare kanta kamar yadda dokar kasa da kasa ta tanada, yayin da wasu kasashe kamar Spain ke zargin aikata kisan kare dangi ga al'ummar Falasdinu.