Ministar harkokin wajen Jamus ta isa birnin Kyiv na Ukraine
April 2, 2025Cikin wani takaitaccen sakon da ta bayar game ziyarar, ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock ta yi gargadin kada Amurka ta biye wa abin da ta bayyana da dabarun da Rasha ke amfani da su a kan rikicinta da Ukraine.
Shugaban Amurka Donald Trump ya sha nanata wasu matakan rangwanta wa ko ma taimaka wa takwaransa na Rasha wato Vladimir Putin.
Sai dai bayanan Amurka ba su kai ga samar da wani sakamako ba a teburin tattaunawa ko kuma a fagen yaki a zahiri ya zuwa yanzu.
Annalena Baerbock ta Jamus ta ce taron ministocin kungiyar tsaro ta NATO da za a yi cikin wannan makon zai fayyace wa Amurka a kan dababrun da take yi a rikicin na RAsha da Ukraine.
Baerbock ta kuma ce Shugaba Putin na Rasha na jan lokaci ne, amma ba mai son zaman lafiya ba ne a wannan rikici.