Wadephul ya isa Isra'ila
July 31, 2025Ministan harkokin wajen Jamus Johann Wadephul ya fara ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Isra'ila, inda ake sa ran wuraren zai zai shiga suka hada da yankin Gabar Yamma da Kogin Jodan da ke karkashin ikon mamaya na Isra'ila.
Karin Bayani: Jamus ta yaba da rawar Jordan kan warware rikicin Gabas ta Tsakiya
Wadephul wanda yanzu haka yake ziyara a yankinGabas ta Tsakiya ya bukaci Isra'ila ta kara bude hanyar kai taimako cikin yankin zirin Gaza na Falasdinu, domin dakile wahalar da mutane suke ciki a yankin.
Ministan harkokin wajen na Jamus Wadephul ya ce matsalolin da ake fuskanta na kai kayan agaji zuwa zirin Gaza, suka janyo kasashe da dama ke neman amincewa da 'yancin yankin Falasdinu, gabanin kammala tantance iyaka na bangarorin biyu, bisa kudirin kasashen duniya.