Mike Waltz zai ajiye mukaminsa
May 1, 2025Mike Waltz da mataimakinsa Alex Wong su ne Jami'ai na farko da za su bar aiki a majalisar gudanarwar shugaba Donald Trump 'yan kwanaki bayan cikarsa kwanaki 100 a karagar mulki.
A watan Maris Waitz ya ayyana daukar alhakin kuskuren da ya faru, da aka sanya sunan wani dan jarida cikin jadawalin mutanen da ake aike wa sakonni inda manyan jami'an gwamnatin Trump ke tattauna hare haren da sojoji ke kaiwa a Yemen.
Waltz ya ce bai san babban editan mujallar The Atlantic Jeffrey Goldberg ba inda ya kara da cewa bai san yadda aka yi sunansa ya shiga cikin jerin mutanen da aka aike wa sakon sirrin ba.
A lokacin Trump ya sassauta batun inda ya ce ba wani abu ne muhimmi ba, ya kuma yi alkawarin ci gaba da goyon bayan Waltz.
Babu dai tabbas a game da ko wanene zai maye gurbin tsohon dan majalisar dokokin na Republican mai shekaru 51 a duniya da ya fito daga jihar Florida.
Wasu dai sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa mai yiwuwa ya kasance Steve Witkoff wakilin Trump a Gabas ta Tsakiya da yakin Ukraine.