Merz ya roki Netanyahu ya kawo karshen yunwa a Gaza
July 27, 2025Shugaban Gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya sake yin magana ta waya da Firamistan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, inda ya bukace shi da ya yi duk mai yiwuwa domin rage mummunan halin jin kai da ake ciki a Gaza.
Shugaban gwamnatin ya bayyana damuwarsa matuka game da mummunar matsalar jin kai da ke faruwa a Gaza.
Lokaci ya zo da za a kawo karshen yakin Gaza - Merz
Ya kuma kira Netanyahu da ya yi duk abinda zai iya yi don a cimma tsagaita wuta nan take a Gaza
Mai magana da yawun gwamnatin Jamus, Stefan Kornelius ya fada a ranar Lahadi cewa mista Merz ya kuma bukaci Netanyahu da ya nuna halin tausayi ga mutanen Gaza.
Jamus ta gargadi Isra'ila da ta guji fushin abokan huldarta
Kasashen duniya na kara matsa wa Isra'ila lamba ta kawo karshen rikicin Gaza musamman ganin yadda yunwa ke kassara mazauna zirin.