SiyasaJamus
Merz ya bukaci garanbawul ga tsarin tallafi
August 23, 2025Talla
Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya yi kiran yin garanbawul ga tsarin tallafin jin dadi da walwalar al'umma wanda gwamnati ke kashe makudan kudade yayin da a waje guda ya ce gwamnatin ba za ta yi karin haraji ga matsakaitan kamfanoni ba.
Kalaman shugaban gwamnatin wanda ya yi taron Jam'iyyarsa ta CDU a jihar Lower Saxony a ranar Asabar na iya share fagen takaddama da kawancen jam'iyyun da ke cikin gwamnatinsa musamman Jam'iyyar SPD
Tun da farko dai kawancen gwamnatin sun amince da yin gyara ga tsarin Inshora kan walwalar jama'a wanda ya kunshi tsarin lafiya da Fansho da tallafi ga wadanda basu da aiki. Kwaskwarimar ta biyo bayan tsadar rayuwa da kuma gibi a kasafin kudin gwamnati.