Merz na Jamus zai gana da Trump na Amurka
May 31, 2025Shugaban Gwamnatin Jamus Friedrich Merz zai gana da shugaban Amurka Donald Trump a ranar Alhamis mai zuwa a fadar White House domin tattauna batutuwa da suka shafi kasuwanci da tattalin arziki.
Shugabannin biyu za kuma su tauna rikice-rikicen Gabas ta Tsakiya da kuma Ukraine a yayin da Trump din ke kokarin ganin an samar da yarjejeniyar zaman lafiya.
Jamus: Merz ya gaza samun amincewar majalisa
Ziyarar ta mista Merz za ta kasance ta farko zuwa wajen Turai tun bayan shiga ofis a farkon watan Mayu, kuma wannan shi ne karon farko da shugabannin biyu za su yi ganawar keke da keke.
Shugabannin za kuma su tattauna dangantaka tsakanin kasashensu kamar yadda kakakin gwamnatin Jamus Stefan Kornelius ya fada a ranar Asabar.
Kalubalen sabuwar gwamnatin Jamus
Shugaba Trump dai ya dankara wa Turai haraji da kuma fada mata ta tsaya kan kafafunta a harkar tsaro tun bayan komawarsa fadar White House a matsayin shugaban Amurka.