Hamas: Menene ra'ayin Isra'ilawa kan Gaza?
August 13, 2025Yayin da Isra'ila ke ci gaba da shirinta na mamaye Zirin Gaza gaba dayansa, gwamnatin Benjamin Netanyahu na fuskantar karin suka daga cikin gida. A karshen mako, Isra'ila ta shaida gagarumar zanga-zangar da ke zaman guda cikinwa wadanda aka taba yi kan yakin da take ci gaba da yi a Gaza, inda dubban Isra'ilawa suka fito kan tituna suna nuna bacin ransu. Har yanzu akwai kimanin Isra'ilawa 50 a hannun kungiyar Hamas a Zirin Gaza, kuma iyalansu suna jin tsoron cewa shirin Netanyahu na kwace iko da yankin zai kara jefa rayuwar 'yan uwansu cikin hadari.
Karin Bayani: Shin me ya saka Saudiyya shiga gaba kan samar da 'yancin Falasdinu?
Gil Dickmann dan uwan wata mata ce da ta mutu a hannun Hamas mai suna Carmel Gat ya shaida wa DW cewa, yanke shawarar mamaye karin kasa zai jefa rayuwar sauran wadanda Hamas din ke garkuwa da su da suka rage a hannunta cikin hadari. Ita ma Naama Shueka 'yar uwar matashi Evyatar David da ke hannun Hamas da aka gani a rame a wani bidiyo da Hamas ta fitar kwanan nan ta ce, hanya daya tilo da za ta dawo da su da rai ita ce cimma yarjejeniyar sako su. Sannu a hankali yawan Isra'ilawan da ke goyon bayan iyalan wadanda Hamas ke garkuwa da su na karuwa. Binciken da Cibiyar Dimukuradiyyar Isra'ila (IDI) ta gudanar, ya nuna yadda ra'ayin jama'a ya sauya.
A tsakiyar watan Oktoban 2023, jim kadan bayan harin Hamas na bakwai ga Oktoba kan Isra'ila, kaso 17 cikin 100 ne kacal na Isra'ilawa suka ce gwamnati ta shiga tattaunawa domin sakin wadanda Hamas din ta kama ko da hakan na nufin a dakatar da fada. Amma shekara guda bayan harin, kaso 53 cikin 100 sun amince da irin wannan ra'ayin. Ko da yake mafi yawan Isra'ilawa suna so a dawo da mutanen da ke hannun Hamas ne da kuma ceton rayuwar sojojinsu, amma ba wai suna tausayin Falasdinawa ba ne ko kuma son kasancewa tare da su kamar yadda wani bincike ya gano. Wani binciken da Cibiyar Dimukuradiyya ta Isra'ila IDI ta gudanar a karshen watan Yuli a kan ko Isra'ilawan sun damu da halin yunwa da ake ciki a Falasdinu, ya nuna cewa kaso 79 cikin 100 ba su nuna damuwa ba.
Karin Bayani: Isra'ila da Hamas sun cimma tsagaita wuta a Gaza
Wani marubucin Isra'ila Etgar Keret ya shafe watanni yana zanga-zanga, kan abin da gwamnatin Netanyahu ke yi a Gaza ya kuma nuna farin ciki da ganin karin 'yan Isra'ila sun bi sahunsa. Keret ya kuma yi kokarin bayyana dalilin da yasa Isra'ilawa, ba su damu sosai da halin da Falasdinawa ke ciki ba. A cewarsa, irin labarai da ake yadawa a kasar a baya da kuma na makonnin nan sun sha bam-bam musamman a kan halin da ake ciki. Masu nazarin ayyukan kafafen yada labarai a Isra'ila suna jaddada cewa, kaso 40 cikin 100 na Isra'ilawa ne ke kallo labarai a talabijin. A yayin da kashi 78 cikin 100 ke amfani da shafukan sada zumunta, inda ake yada rahotanni da hotuna na halin da ake ciki a Gaza.