Medvedev ya zama firaministan Rasha
May 8, 2012Majalisar dokokin Rasha ta amince da Dimitry Medvedev da ke zama tsohon shugaban ƙasa a matsayin firaminista kamar yadda shugaba Putin ya bukata. 'Yan majalisa 299 daga cikin 443 da suka kaɗa ƙuri'a ne suka albarkanci naɗin Medvedev kwana guda bayan miƙa mulƙi da ya yi ga hannun Vladimir Putin, wanda ya riƙe muƙamin firamiya lokacin da Medvedev ya ke riƙe da madafun iko.
Wannan canjin matsayi da shugabannin biyu suka yi ya haddasa zanga-zangar nuna rashin amince a titunan birnin Moscow . Mutane sama da 20 ne 'yan sanda suka tsafke ciki kuwa har da shugabannin jam'iyun adawa biyu da suka halarci zangar zangar da ta gudana a kusa da fadar mulki ta Kremlin da nufin yin Allah wadai da babakere da Putin da Medvedev ke yi a harkokin mulkin Rasha.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu